Shugabannin hamayya na kasar Libya dake da karfin iko a birnin Bengazhi, su na muhawara kan ko zasu nemi taimakon kasashen waje domin kai hari ta sama a kan cibiyoyin sojin shugaba Moammar Gadhafi da wadansu muhimman cibiyoyi. Jami’ai na majalisar gudanarwa ta Benghazi sun bayyana jiya Talata cewa, watakila ba za a taba kawo karshen arangama da ake yi da dakarun dake goyon bayan Gadhafi ba, idan har kasashen waje ba su kai farmaki ta sama tare da kakabawa Gaddafi takunkumi ba. Jaridar Washington Post ta ambaci wasu membobi uku na kwamitin na cewa, zasu nemi taimakon kai hari ta sama nan ba da dadewa ba, sabanin matsayinsu na baya cewa, ba zasu nemi taimakon sojojin kasashen ketare ba. Suka ce ba su bukatar sojojin kasashen waje su taka cikin Libya. Majalisar gudanarwar da ‘yan hamayya suka kafa ta kunshi lauyoyi, da ‘yan boko, da alkalai da kuma wadansu manyan masu fada a ji. ‘Yan tawayen kasar Libya da suka gana da jami’an amurka a birnin Washington cikin wannan makon sun yi irin wannan kiran na neman goyon baya daga dakarun Amurka da kuma na kungiyar kawancen tsaro ta NATO, da ya hada da yiwuwar kai harin soji kan mayakan saman Mr. Gadhafi da kuma tankoki da dakarunshi. Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta tabbatar da cewa, Amurka ta gana da kungiyoyin hamayya na kasar Libya da dama a Washington cikin wannan makon, sai dai bata bada karin haske ba. Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice tace za a yi riga mallam masallaci idan aka fara tattauna batun ba ‘yan hamayya tallafin soja yayinda bangarorin daban daban suke kokarin hada kai.
Shugabannin hamayya na mawahara kan yiwuwar neman tallafin soji daga kasashen ketare.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024