Sarki Abdallah na Saudiyya ya kara yawan kudin da ake kashewa a kasar kan abubuwan more rayuwa, bayan dawowarsa kasarsa a yayin da ake ta tawaye a duniyar Larabawa.
Abubuwan maore rayuwar da aka bayyana su yau Laraba sun hada da wani kudin bayar da tallafin bashin gina gida na dala biliyan 11, da kuma wasu biliyoyin daloli na inganda sauran abubuwan maore rayuwa das u ka hada da kudaden biyan wutar lantarki da ruwa dag yare-gyaren gidaje da habbaka ilimi da sauransu.
Sarki Abdallah ya kuma bayar da umurnin karin albashi ga ma’aikatan gwamnati da 15%.
Sarki Abdalla ya isa Saudiyya yau Laraba bayan ya yi watanni uku yana jinya a kasar waje.
Sarki dan shekaru tamanin da wani abu ne. A watan Nuwamba an masu aikin tiyata a birnin New York. An kuma masa wani aikin na mataki na biyu a watan Disamba.