Yau birni na biyu mafi girma a duk kasar New Zealand, wanda ake kira Christchurch, yana kwance male-male, duk kusan gine-ginen dake cikinsa suna a kasa, sun rushe a sanadin wata gagarumar girgizan kasan da ta rafgangar za hatta wuraren ibada, wacce kuma ta abku a daidai lokacinda ake cikin mafi hada-hadar ma’aikata.
Girgizan ta hallaka mutane da dama, kuma wasu da yawa sun salwanta, ana nemansu yayinda masu aikin kawo ceto dake aiki da manyan injuna suke ci gaba da farfasa kasar da ta fadi a kokarin neman mutanen da ginepginen suka danne.
Rahottanin dake fitowa daga inda abin ya afru na cewa da kyar ne idan girgizan bai halakka mutanen da yawansu ya kai 300 ba – ko da yake hukumomi na taka-tsatsan bada alkalumman, suna cewa yawan matattun na tsakanin 38 ne zuwa 65 – wanda shine yawan ainihin gawawwakin da aka gani kuma aka kirga.