Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Kama Wani Dan Kasar Saudiyya Kan Zargin Ta'addanci

Khalid Aldawsar dalibi daga Saudiyya da hukumomi suka kama kan zargin ta'addanci.
Khalid Aldawsar dalibi daga Saudiyya da hukumomi suka kama kan zargin ta'addanci.

An kama wani saurari dan kasar Saudiyya a jihar Texas dake nan Amurka kan zargin makarkashiyar neman cibiyoyi da za’a kai wa harin bomb,ciki har da gidan tsohon shugaban Amurka George W.Bush.

An kama wani saurari dan kasar Saudiyya a jihar Texas dake nan Amurka kan zargin makarkashiyar neman cibiyoyi da za’a kai wa harin bomb,ciki har da gidan tsohon shugaban Amurka George W.Bush.

Hukumar binciken manyan laifuffuka (FBI) tace dan shekaru 20 da haifuwa Khalid Ali-M Aldawsari, ya rubuta cikin kundinsa cewa ya kware da harshen turanci,ya koyi hada nakiyoyi,ya zabi wurare da zai kai wa farmaki,abinda ya rage sai jihadi.

Ranar laraba ce aka kama Aldawsari kan zarginda gwamnatin tarayya take masa na kokarin amfani da makamin kare dangi.

Wata sanarwar ma’aikatar harkokin shari’a ta bayar tace masu bincike suna biye da take-taken Aldawsari a Internet.Masu bincike suka ce Aldawsari ya yi nazarin nakiyoyi,kuma sai ya turawa kansa sakonnin Email kan haka. Ma’aikatar tace cikin irin wadan nan email din har da daya wadda ya lakabawa sunan “Gidan azzalumi” shine gidan tsohon shugaban Amurka Bush.

XS
SM
MD
LG