‘Yan jam’iyyar Republican da ke da rinjaye a Majalisar Dokokin Amurka na shirin gabatar da kudurin doka ta halatta kashe kudi na gajeren lokaci don kau da yiwuwar tsayawar al’amuran gwamnati.
Shugaban Masu Rinjayen Majalisar Dokokin Eric Cantor ya gaya wa manema labarai yau Jumma’a cewa shirin na ‘yan Republican ya hada da biliyan 4 na rarar da aka samu daga rage kashe kudin gwamnati kuma na iya taimakawa wajen tafi da harkokin gwamnati na tsawon sati biyu bayan karin wa’adin kasafin kudi na yanzu ya kare ran 4 ga watan Maris.
‘Yan Republican na matsa wa ‘yan Dimokarat su amince da shirin ko kuma su dau laifi idan al’amuran gwamnati su ka tsaya.
Shekarar kudin bana dai za ta fara ne ran 1 ga watan Oktoba, to amman Majalisa ba ta gabatar da kasafin kudi ba, a maimakon hakan sai ta amince da kashe kudi na gajeren lokaci don tabbatar da cewa ana tafi da harkokin gwamnati.
Kasafin kudin dai wani babban abin takaddama ne tsakanin ‘yan Republican da Dimokarat.