Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Sarakuna Da Su Bada Gudunmawar Ganin Anyi Zabe Cikin Nasara

Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Sarakuna Da Su Bada Gudunmawar Ganin Anyi Zabe Cikin Nasara
Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Sarakuna Da Su Bada Gudunmawar Ganin Anyi Zabe Cikin Nasara

Mai alfarma sarkin Musulmin Najeriya Sultan Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci ‘yan Nigeria da su ci gaba da yin addu’o’i domin samun shugabanni na gari masu tausayin al’umma a babban zaben kasar dake tafe a cikin wannan wata.

NIGER, NIGERIA - Sultan Sa’ad Abubakar wanda yake jawabi wajen bikin nadin sarauta tare da mika sanda ga sabon Sarkin Sudan na Kontagora a Jihar Neja, Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu a karshen wannan mako, ya ce suna gudanar da addu’o’i na musamman domin ganin an gudanar da wannan zabe cikin kwanciyar hankali.

Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya mika sandar girma ga Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu
Gwamnan Jihar Neja Alhaji Abubakar Sani Bello ya mika sandar girma ga Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu

Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu wanda shi ne na bakwai a jerin sarakunan masarautar ta Kontagora da ta samu asali daga Shehu Usman Danfodio ya ce za su yi kokarin kamanta adalci a wannan mulki, sannan ya bukaci hakimansa da daggatai dama masu unguwanni da su tabbatar sun sanya idanu kan jama’a musamman a wannan lokaci da ake fama da miyagun mutane.

Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu.
Sabon Sarkin Sudan na Kontagora Alhaji Muhammadu Barau Mu’azu na biyu.

Gwamnan Jihar Nejan Alhaji Abubakar Sani Bello wanda ya mika sandar mulkin ga sabon sarkin ya bukaci sarakunan Najeriya da su ba da gudummuwar da za ta taimaka wajen ganin an yi babban zaben kasar cikin nasara.

Sauari cikakken rahoto daga Mustapha Nasiru Batsari:

Sarkin Musulmi Ya Yi Kira Ga Sarakuna Da Su Bada Gudunmawar Ganin Anyi Zabe Cikin Nasara.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

XS
SM
MD
LG