Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ga Watan Azumin Ramadan A Najeriya


Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar
Sarkin Musulmi Muhammadu Sa'ad Abubakar

“Hakika mun samu labari na ganin wannan wata, daga shugabanni na addinin musulunci daban-daban, daga jihohi daban-daban, kamar nan jihar Sokoto, jihar Borno, jihar Kano, jihar Kaduna, jihar Katsina, jihar Filato, jihar Zamfara da jihar Yobe."

Majalisar Koli ta Malaman Addinin Islama ta NSCIA a Najeriya ta sanar da ganin watan Ramadana na shekarar 1443 AH a ranar Juma’ar nan.

Hakan na nufin gobe Asabar 2 ga watan Afrilu ya zama daya ga watan Ramadan 1443/2022.

Shugaban Majalisar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar II ne ya ba da sanarwar a daren Juma’ar nan.

“Hakika mun samu labari na ganin wannan wata, daga shugabanni na addinin musulunci daban-daban, daga jihohi daban-daban, kamar nan jihar Sokoto, jihar Borno, jihar Kano, jihar Kaduna, jihar Katsina, jihar Filato, jihar Zamfara da jihar Yobe.

“Kuma mun tabbatar da wannan gani, bayan mun tattauna da wadannan shugabannin, kuma Alhamdulillahi, mun gamsu da da wannan gani da suka aiko mana. Muna kira ga musulmi gobe insha Allahu a tashi da azumin watan Ramadan.” Sultan Sa'ad ya ce.

Kasar Saudiyya ma ta bayyana ganin jinjirin watan na Ramadan, wanda ta ce an gan shi wurare da dama kasar.

XS
SM
MD
LG