KANO, NIGERIA - An haifi marigayi Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi a ranar Juma'a 5 ga watan Janairu na shekarar 1945 a garin 'Yar'gaba dake gefen birnin Dutse fadar masarautar Dutse kuma shalkwatar jihar gwamnatin jihar Jigawa.
Bayan fara koyon karatun Alkur’ani yana dan shekara 4, kana daga bisani aka saka shi a makarantar elemantare a ranar 1 ga watan Afirulu na shekarar 1952 ya shiga ajin share fagen shiga firamare zuwa 1956, sai babbar firamare da ke Birnin Kudu, daga 1957 zuwa 1959.
Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi,ya halarci Jami'ar Ohio ta ƙasar Amurka inda ya samu digiri a fannin hada-hadar Kuɗi daga shekarar 1971 zuwa 1974. Ya kuma yi karatu a jami'ar 'Brandford' da ke ƙasar Ingila a shekarar 1977.
Marigayi ya koyar a Jami'ar Bayero, Kano ya kuma yi aiki a kamfanin (NNDC) da sauran cibiyoyi masu zaman kansu, kana ya zama sarkin Dutse a shekarar 1995.
Wasu daga cikin laffuzan sa na baya-bayan nan, sune akan zabe lokacin daya karbi bakuncin mataimakin babban sifeton ‘yan sandan Najeriya mai kula da shiyya ta daya dake Kano, a fadar inda ya bayyana yakinin sa da fatan gudanar da babban zaben Najeriya cikin lumana da kuma fitar da sakamakon da zai karbu ga kowa da kowa.
Malam Ibrahim Ado Kurawa, marubuci ne, musamman kan sha’anin masarautu wanda ya yi tsokaci akan tarihin masarautar Dutse da kuma salon mulkin marigayi Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, ya ce marigayin ya kawo sauyi ga tsarin tafiyar da harkokin masarautar Dutse, inda ya samar da majalisar Zakka da Hubisi ya gina masallaci da dakin karatu, ya zauna da talakawan sa lafiya, yana cikin sarakunan arewa da ake alfahari dasu saboda yiwa addini hidima.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, gwamnan Jigawa Alhaji Mohammed Badaru Abubakar da tsoffin gwamnonin Jihar, Alhaji Sule Lamido da Ibrahim Saminu Turaki da kuma Barriister Ali Sa’ad Birninkudu kana da Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, Jami’an gwamnati da sauran al’umar Musulmi ne suka halarci sallar jana’izar.
Saurari cikakken rahoto daga Mahmud Ibrahim Kwari: