Rahotanni daga fadar Buckingham na cewa, Sarauniya Ingila Elizabeth ta II ta rasu tana da shekaru 96.
Shekarun Sarauniya Elizabeth 70 akan karagar mulki. Ta karbi mulkin ne bayan mutuwar mahaifinta George VI, a shekarar 1952.
Sarauniyar ta yi aiki da Firaiminista 15 a lokacin mulkinta, inda ta fara da Winston Churchhill.
Ta taimaka wajen yi wa kasarta shugabanci wajen farfadowa bayan yakin duniya na biyu da kuma lokacin yakin cacar baka, da lokacin rikici a arewacin Ireland, da kuma lokacin da aka kafa kungiyar tarayyar turai da ficewar kasar a kungiyar.
Da yawa daga cikin ‘yan kasar na kallon Sarauniya Elizabeth a matsayin ginshikin kasar ta Birtaniya a daidai lokacin da wasu ke ganin tagomashin kasar na dishewa a idon duniya.