Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jinjina dadewar da marigayi Yarima Philip da Sarauniyar Ingila Elizabeth suka yi a matsayin ma’aurata.
A shekarar 1947 Duke of Edinburg, Philip da sarauniya Elizabeth suka yi aure.
Philip ya rasu ne a ranar Juma’a, yana da shekara 99.
“Shugaba Buhari ya jinjinawa Duke of Edinburgh, a matsayin miji na kwarai wanda ya yi zaman lafiya a aurensa da Sarauniya Elizabeth tun daga shekarar 1947.” Buhari ya fada a wata sanarwa da kakakinsa Malam Garba Shehu ya fitar, don mika sakon ta’aziyyarsa ga masarautar Burtaniya bisa rasuwar Philip.
“Wannan abin alfahari ne ga duk auren da ya yi irin wannan dadewa a kowane mataki.”
Buhari na mika sakon ta’aziyyarsa ne ga Sarauniya Elizabeth kan rasuwar mijin nata Yarima Philip.
“Yarima Philip na daya daga cikin fitattun mutane da kasashen duniya suka san irin gudunmowar da suka bayar, wajen tallafawa kasashe da Ingila ta rena (Commonwealth) wanda ba za’a manta da shi ba.”
Ya kara da cewa, “Yarima Philip mutum ne jarumi, wanda ya ba da gudunmowa a fannonin ayyukan al’uma da kare halittun dazuka da tallafawa matasa a kasahe sama da 130.”
“Shugaban yana mika sakon ta’aziyyarsa ga gwamnatin Burtaniya, da mambobin kungiyar kasashen da Ingila ta rena, bisa wannan abin alhini na rashin wannan basarake kuma jarumi a idon duniya.”
A shekarar 2017 Yarima Philip ya yi ritaya daga ayyukan masarautar
Bayan shekara daya, ya gamu da wani mummunan hadarin mota a lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa gidan iyalan masarautar ta Ingila da ke Sandringham.
Lokaci na karshe da aka gansa a baina jama’a, shi ne a watan Yulin shekarar 2020 a fadar masarautar ta Windsor Castle.