Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Liz Truss Ta Zama Sabuwar Firaiministar Birtaniya


Liz Truss
Liz Truss

Truss da tsohon Sakataren Baitul Malin kasar Rishi Sunak ne suka fafata a kokarinsu na maye gurbin Firaiminista Boris Johnson.

Jam’iyyar Conservative a Birtaniya ta ayyana Sakatariyar harkokin wajen kasar a matsayin wacce ta lashe zaben cike gurbin shugaban jam’iyyar, abin da ke nufin ita ce sabuwar Firaiminitar kasar.

Truss da tsohon Sakataren Baitul Malin kasar Rishi Sunak sun fafata a kokarinsu na maye gurbin Firaiminista Boris Johnson.

A watan Yuli Johnson ya sanar da cewa zai yi murabus bayan da gwamnatinsa ta yi fama da wasu abubuwan kunya da suka faru.

An taba samun Johnson da laifin karya dokar kulle da gwamnatinsa ta saka don takaita yaduwar cutar COVID-19.

Daga cikin kalubalen da ake hangen Truss za ta fuskanta, akwai matsalar komadar tattalin arziki da Burtaniya ke fama da ita, lamarin da ya sa al’umar kasar suke ganin tashin farashin kudaden makamashi.

A ranar Talata, Truss za ta kai ziyara Scotland a cewar kamfanin dillancin labarai na AP, inda Sarauniya Elizabeth za ta gayyace ta don sharar fagen kafa gwamnati.

XS
SM
MD
LG