Amurka ta sabunta gargadin da ta yi ma Amurkawa na gujewa yin tattaki zuwa Najeriya, makonni uku a bayan da mutane 12 suka mutu a tagwayen hare-haren bam da aka boye cikin mota a Abuja, babban birnin kasar.
Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta gargadi Amurkawa da su guji yin tattaki zuwa wasu jihohi 9 daga cikin 36 na Najeriya idan ba wai hakan ya zamo dole ba a saboda kasadar fadawa hannun masu sace mutane ko 'yan fashi ko kuma hare-hare da makamai.
Gargadin yace tsagera da 'yan daba sun sace 'yan kasashen waje fiye da 111 tun daga watan janairun 2009 zuwa yanzu. An kashe 6 daga cikin wadannan mutanen da aka sace.
Har ila yau ta ce barayi da 'yan fashi da 'yan daba da wasu dake batar da kama ta hanyar shiga kayan 'yan sanda su na aikata munanan laifuffuka matsala ce da ta zamo ruwan dare a fadin Najeriya. Sanarwar ta shawarci Amurkawa da su gujewa fita daga cikin manyan birane idan dare yayi.
Wani wanda ya ce shi kakakin kungiyar MEND ne ya dauki alhakin kai hare-haren bam na ranar 1 ga watan Oktoba a Abuja. Daga baya wasu shugabannin kungiyar sun ce babu hannunsu a ciki.
A ranar jumma'a wannan da ta shige, shi wannan kakaki na MEND ya ce kungiyarsu tana shirin kai wani harin a cikin wannan wata a Abuja.
Wuraren da Amurka ta gargadi 'yan kasarta da su gujewa sune jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Delta da kuma Rivers a yankin Niger Delta; da jihohin Abia, Edo da Imo a yankin kudu maso gabas, sai jihohin Bauchi da Borno a yankin Arewa maso gabas da kuma garin jos a Jihar Filato.