Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Barack Obama Ya Dauki Alhakin Kayen Da Aka Yi Ma Jam'iyyar Democrat


Shugaba Barack Obama yana amsa tambayoyin 'yan jarida game da zabe, laraba 3 Nuwamba 2010 a fadarsa ta White House
Shugaba Barack Obama yana amsa tambayoyin 'yan jarida game da zabe, laraba 3 Nuwamba 2010 a fadarsa ta White House

Shugaban yace faduwar da jam’iyyar Democrat ta yi, ta nuna bacin ran Amurkawa kan tattalin arzikin da ya kasa farfadowa har yanzu, da kuma rashin aikin yi da yayi tsanani

Shugaba Barack Obama na Amurka ya yarda cewa jam’iyyarsa ta sha kashi a zabubbukan ‘yan majalisar dokokin da aka yi shekaranjiya talata a nan Amurka, yana mai fadin cewa faduwar da jam’iyyar Democrat ta yi, ta nuna bacin ran Amurkawa kan tattalin arzikin da ya kasa farfadowa.

A lokacin da yake hira da manema labarai jiya laraba a fadarsa ta White House, Mr. Obama ya dauki alhakin tafiyar hawainiyar da ake samu wajen farfado da tattalin arzikin, ya kuma lashi takobin cewa zai yi kokarin samo hanyar daidaitawa da ‘yan Republican.

‘Yan Republican sun kwace majalisar wakilai ta tarayya daga hannun jam’iyyar Democrat ta Mr. Obama, sun kuma samu karin kujeru a cikin majalisar dattijai, koda yake har yanzu ‘yan Democrat ke da rinjaye a majalisar dattijan.

Shugaba Barack Obama
Shugaba Barack Obama

Mr. Obama yace babu wata jam’iyya guda da zata iya shata alkiblar kasa ita kadanta. Ya yarda cewa zai yi wuya ya iya gabatar da shirye-shiryensa ba tare da goyon bayan ‘yan jam’iyyar Republican ba, amma yace ya kosa ya ji irin ra’ayoyin da ‘yan Republican suke da su kan yadda za a kara samar da ayyukan yi tare da farfado da tattalin arziki.

Ana sa ran John Boehner zai zamo kakakin majalisar wakilan tarayya idan sabuwar majalisar ta fara aiki a watan Janairu. Boehner yace babban gurin jam’iyyarsu ta Republican shi ne samar da ayyukan yi da rage yawan kudaden da gwamnati take kashewa.

XS
SM
MD
LG