Mafi aksarin wannan matsala ta rashin tsaro ta fi addabar yankin arewa maso gabashin kasar ne musamman a jihohin Borno da Yobe, sai kuma jihar Adamawa.
Baya ga asarar rayuka da aka yi a wannan lamari mai cike da sarkakiya, rikicin ya yi tasiri kwarai akan harkokin kasuwancin yankunan da kuma harkar ilimi.
Yanzu haka dubun dubanta yara kanana da dama ne ba sa zuwa makaranta saboda rashin tsaro a yankunansu, lamari da ya sa suke ta galantoyi akan tituna yayin da suke zaune a sansanonin ‘yan gdun hijra da hkumomi suka samar.
Ganin cewa harkar ilimi batu ne mai mahimmanci musamman ga yara kanana, wata kungiya mai zaman kanta da ake kira Creative Associates International da ke birnin Washington a Amurka, wacce kuma ke samun tallafi daga hukumar tabbatar da raya kasashe ta USAID, ta kirkiro wasu wurare da ake koyar da yara ilimin zamani.
Baya ga haka akwai kungiyoyi irin su Red Cross da ke tallafawa, ibda suma sukan sun baiwa wasu mata da suka rasa mazanjensu a wannan rikicin jari domin su fara kasuwancin da zai rike su.
Domin jin yadda makarantar ke gudana da kuma yadda matan da ake tallafawa suke neman taro da sisi, saurari wannan fassarar rahoto da wakilin Muryar Amurka Michael Lipin ya hada mana: