.Bangorin biyu sun tattauna ne kan batutuwa da suka shafi tsaro da ci gaban kasar ta Kamaru da kuma yadda kasashen biyu za su kara dankon zumuncinsu.
Yayin da yake ganawa da manema labarai , Mr Roza ya ce batun Boko Haram da ke ta da kayar baya abu ne da za a shawo kansa.
Dangane da batun dakarun Amurka da aka tura zuwa kasar ta Kamaru, Mr. Roza ya gayawa manema labarai cewa ya gamsu da irin matsugunin da aka basu.
“Na gamsu da matsagunin da aka baiwa dakarun tsaron mu a garin Garwa domin kaiwa ‘yan ta’addan Boko Haram hari akan iyakoki makwabta.”
Yanzu haka dakarun Amurka 300 sun kammala isa kasar inda tuni suka fara aiki akan iyakoki kasar.
Domin karin bayani saurarin rahoton wakilin Muryar Amurka Awwal Garba: