Jamhuriyar Kamaru tana kara karfafa tsaro a jihar Arewa mai Nisa, musamman a bakin iyaka da Najeriya, domin dakushe irin hare-haren da 'yan Boko Haram suke tsallakowa daga Najeriya su na kaiwa.
Kasar ta Kamaru ta yi hasarar sojojinta kimanin 60 a wannan yaki da ake yi da 'yan Boko Haram, wadanda a bayan da aka wargaza su daga sansanoninsu, suka sauya salo su na kai hare-haren sari-ka-noke, ko kuma amfani da yara kanana wajen kai hare-haren kunar-bakin-wake.
Wadannan hare-haren sun sanya manoma dake jihar Arewa mai Nisa cikin wani mummunan hali a saboda fargaba. Da yawansu, ba su shuka komai ba a daminar bana, yayin da wasu da suka shuka din ma suka kaurace ma gonakinsu.
Wannan al'amari ya janyo tsadar kayayyakin masarufi a jihar, abinda ya sa har gwamnan jihar, Mijinyawa Bakary, yake cewa jama'a masu yawea zasu tsinci kawunansu a cikin wani yanayi na ni 'ya-su a saboda rashin kayan abinci.
Gwamna Bakary ya fadawa manema labarai a ofishinsa dake garin Maroua cewa mutanen jihar da na sauran sassan arewacin Kamaru su na samun akasarin kayayyakin masarufinsu ne daga Najeriya, amma wannan rikici na Boko Haram ya hana manoma da 'yan kasuwa sakat, domin ya dakatar da harkar saye da sayarwa tsakaninsu kasashen biyu baki daya.
Ya roki hukumomin Kamaru da su dauki matakan agazawa al'ummar yankin.