Da kakausan harshen Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta la’ani shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo bayan da a ranar alhamis sojojin kasar suka bude wuta akan masu zanga zangar harma suka kashe mata bakwai. A jiya juma’a Hillary Clinton tace Laurent Gabagbo da sojojinsa basu damu da rayukan mutane. Ta baiyana Mr Gabagbo a zaman wanda ke son kansa, tace bai damu da cewa yunkurinsa na ci gaba da makalewa akan mulki duk kayin daya sha a zaben da aka yi a kasar yasa ana zaman tankiya a kasar ba. Yawancin kasashen duniya sun dauki Alassane Ouattara a zaman mutumin daya lashe zaben da aka yi a watan nuwamba, to amma Mr Gbagbo yaki ya bada kai. A jiya juma’a wani kwamitin shugabanin kasashen Afrika yayi wani taro a Nuwakchott baban birnin kasar Mauritania a wani kokarin samun hanyar magance cijewar siyasa a Ivory Coast. Kwamitin yayi niyar zuwa Ivory Coast domin yaci gaba da shiga tsakani amma kuma ya soke wannan ziyara. Kamfanin dilancin labarun Faransa ya bada labarin cewa kwamitin ya bukaci nan da nan a kawo karshen kashe kashe da zanga zangar a Ivory Coast, domin kuwa idan ba’a yi hankali ba suna iya bugewa da zama tarzoma.
Da kakausan harshen Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta la’ani shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo bayan da a ranar alhamis sojojin kasar suka bude wuta akan masu zanga zangar harma suka kashe mata bakwai. A jiya juma’a Hillary Clinton tace Laurent Gabagbo da sojojinsa basu damu da rayukan mutane
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024