Shugaban kasar Ivory Coast mai ci yanzu Laurent Gbagbo ya sanar da cewar gwamnati zata karbi aikin sayar da koko da kuma kofi a kasashen ketare. Dokar da aka karanta a tashar talabijin ta kasar Jiya Litinin tace gwamnati ko kamfanin da gwamnati ta amince da shi ko kuma wanda gwamnati ta ba lasisin kadai ke da izinin sayar da kofi ga ‘yan kasashen ketare. Kasar Ivory Coast ce kan gaba wajen noma koko a duniya, kuma farashin ya yi tashin gwauron zabo fiye da yadda aka taba gani cikin shekaru talatin, tunda aka fara takaddama a kan zabe cikin watan Nuwamba. Mr. Gbagbo ya ki amincewa da sakamakon zaben ya kuma ki mika mulki ga Alassane Ouatarra wanda Majalisar Dinkin Duniya tace shine ya lashe zaben. Saura mako guda kafin cikar wa’adin dakatar da saida koko da Mr. Ouattara ya diba. An nemi dakatar da saida kokon ne da nufin toshe hanyar samun kudin Mr. Gbagbo. Jiya Litinin har wa yau, ‘yan tawaye dake goyon bayan Ouatarra suka ce sun kwace gari na uku daga hannun dakarun dake goyon bayan Mr. Gbagbo. Yan tawayen sun ce sun kwace garin Toulepleu dake yamma, a wani kazamin fada da aka yi ranar lahadi. Makon da ya gabata, ‘yan tawayen suka kwace wasu garuruwa biyu a yammacin Ivory Coast. Dakarun dake goyon bayan Mr. Gbagbo sun ce zasu maida martani
Shugaban kasar Ivory Coast mai ci yanzu Laurent Gbagbo ya sanar da cewar gwamnati zata karbi aikin sayar da koko da kuma kofi a kasashen ketare
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024