Ita wannan zanga-zangar lumana ta goyon bayan Gwamnatin Angola an yita ne ‘yan kwanaki kadan kafin gudanar da wata zanga-zangar kin jinin Gwamnatin da wasu suka shirya yinta ta amfani da na’urar aikewa da sakonni ta ‘Intanet’ da aka shirya fara turawa jama’a tun daga gobe litinin. Kasar Angola kasa ce dake da arzikin lu’u-lu’u da man fetur, amma al’ummar kasar sai fama suke da fatara da talauchi.
Magoya bayan Gwamnatin kasar Angola sun yi zanga-zangar nuna goyon bayan shugaba Jose Eduardo dos Santos
Rahotanni daga kasar Angola na cewa dubban ‘yan kasar sun yi dafifi da cincirindo a kan titunan Luanda jiya Asabar domin zanga-zangar lumana ta nunawa shugaba Jose Eduardo dos Santos kauna da goyon baya.