Daruruwan masu zanga zanga wadanda ke jin takaicn yadda gwamnitocin baya na Masar suke take hakki da yancin jama’a sunyi kokarin su kutsa ginin hukumar tsaron cikin gida a birnin Alexandria a jiya juma’a duk da cewa masu zanga zangar a birnin Alhakira sunyi maraba da sabon Prime Minista Eassam Sharaf. Mr Sharaf ya fadawa taron mutane a dandalin Tahrir cewa yana aiki ne domin biyan bukatun jama’ar kasar. A ranar alhamis gwamnatin rikon kwaryar kasar ta nada Mr Sharaf wanda anan Amirka yayi karatu. Ya yi dan jawabi a jiya juma’a a dandalin Tahrir inda mutane ke taruwa a duk juma’a domin bukatar sauye sauyen harkokin siyasa dana tattalin arziki. Yace yana son yaga kasar Masar inda jami’an tsaro zasu yi aiki domin kare lafiya da dukiyar mutane. A halin da ake ciki jami’an sojan Masar sun bada sanarwar cewa a ranar sha tara ga wannan wata na Maris idan Allah ya kaimu za’a yi zaben jin ra’ayi akan yiwa tsarin mulkin kasar gyare gyare.
Daruruwan masu zanga zanga wadanda ke jin takaicn yadda gwamnitocin baya na Masar suke take hakki da yancin jama’a sunyi kokarin su kutsa ginin hukumar tsaron cikin gida a birnin Alexandria a jiya juma’a duk da cewa masu zanga zangar a birnin Alhakira sunyi maraba da sabon Prime Minista Eassam Sharaf.