Shugaba Barack Obama na Amirka yayi Allah wadai da tarzomar da take faruwa a Ivory Coast.
A wata sanarwar da ya bayar jiya Laraba, shugaba Obama yace musammam yana jin takaicin abinda ya kira kashe farar hula wadanda basa dauke da makamai babu gaira babu dalili, yawancinsu kuma mata a lokacinda suke zanga zangar cikin lumana.Yace yunkurin Mr Gbagbo na ci gaba da kasancewa akan mulki watanni bayan ya sha kaye, tamkar hari ne akan yancin yan kasar.
A makon jiya jami’an tsaro suka kashe mata bakwai a lokacinda suke zanga zanga ciki lumana a birnin Abuja. A ranar talata shedu gani da ido suka cewa jami’an tsaro sun kashe mutane hudu kusa da wani wuri da aka yi jerin gwano.
A halin da ake ciki kuma, masu shiga tsakani a rikicin na Ivory Coast suna shirin ganawa da Alassane Ouattara, a lokacin taron kungiyar kasashen Afrika a Ethiopia.
Wani mai magana da yawun Ouattara yace Mr. Ouattara tuni ya tashi daga Abidjan zuwa birnin Addis Ababa inda ake sa ran a yau alhamis zai gana da wakilan kwamitin daya kunshi shugabanin kasashen Afrika biyar.
Shi dai Mr Gbagbo bai zai halarci taron na Ethiopia amma ya tura wakilansa.