Ma’aikatar harakokin wajen Amurka tace tattaunawar tasu zata mai da hankali ne akan yadda za’a rage tashin hankali, fadada daman kai kayan agaji ga mutanen Syria da kuma neman hanyar warwaren wannan yakin basasa da yaki karewa.
Kerry da Lavrov sun hadu a lokuta da dama makwanni biyu da suka wuce a Geneva da kuma a taron manyan kasashe na G20 a China, amma har yanzu an kasa cimma matsaya kan tsagaita wutar.
Jami’an diplomasiya na Amurka sun zanta da Murayar Amurka kuma sun bayyana rashin jin dadinsu da takwarorinsu na Rasha wanda suke zarginsu da mai da hannun agogo baya akan wasu muhimman baututuwa da aka dace a kansu a cikin wannan lokaci.
Rasha dai itace babban kawar gwamnatin Syria a cikin yakin, a papatawa da take yi da kungiyoyin yan tawaye da IS masu kokarin hambarar da gwamnatin shugaba Assad.
Ita dai Amurka tana goyon bayan yan adawa ne tare kuma da zargin Rasha da da kara dagula a’amura a Syria.