Cibiyar auna girgizara kasa ta Turai tace karfin girgizan ya kai karfi ma’aunin maki biyar a yayid da Amurka kuma tace ya kai maki 5 da digo 3. Gwamnatin ta Amurka tace girgizan kasan ta faru ne a bisa fakon sararin kasa, yayinda girgizar kasa ta Allah da Annabi takan faru ne a karkashin kasa ne.
Wani jam’in Korea ta Kudu ya shaidawa kampanin dillancin labarai na Yonhap cewa a kwai alamar an gwada makamashin nukiliya ne kuma shine ya janyo girgizan kasa, koda yake babu wata sanarwa kan haka da aka bada a hukumance.
Yau Juma’a ce Korea ta Arewa ke shagalin kahuwar kasar kuma galibi a irin wannan ranar ce Koriya take gwajin sababbin makamanta na nukiliya da makaman nukiliya masu lizzami.
Wasu hotunan taurarin dan adam da fasaha sun nuna an samu Karin harkoki a dab da wannan masana’atar sarrafa makaman nukiliya ta Korea ta Arewar dake Punggye-ri inda a nan ne ta gwada makami na hudu a cikin watan Janairu wanda hakan ya sabawa kudirin kwamitin tsaron Majalisar dinkin duniya.
Korea ta Arewa ta dade tana barazanar kai farmaki da makaman nukiliya akan kasashen da take kallo a matsayin makiyanta kamar Korea ta Kudu da Amurka