Amurka tace, jirgin saman mayakan nata smafurin P-8A yana gudanar da aikinsa a sararin sama na kasa da kasa ne, lokacin da jirgin yakin Rasha kirar SU-27 ya wuce kimanin mita uku da shi, babakeren da ya dauki mintoci goma sha tara.
"Jiragen sama da na ruwan mayakan ruwan Amurka, sukan gamu da na Rasha a yankin, kuma galibin lokaci babu wani hadari, kuma ana yi cikin kwarewar aiki, bisa ga cewar ma’aikatar tsaron Amurka. “Sai dai muna da damuwa idan aka sami shawagi mai hadari irin wannan. Wannan na iya janyo zaman dar-dar, kuma yana iya kai ga kuskure ko kuma hadari”.
Ma’aikatar tsaron Rasha tace ta tura jirgin yakinta ne bayanda jirgin saman Amurka ya tunkari kan iyakar Rasha ya kuma kashe na’urar da ake amfani da ita wajen tantance jirage.