Hukumar tace adadin da aka samu daga sansanin da take kula da shi, ya nuna rabin wadanda suka rasa matsugunansu daga Hama sun isa lardin Idlib dake karkashin ‘yan tawaye.
Sauran kuma sun nufi birnin Hama dake karkashin gwamnati, inda aka maida masallatai hudu matsugunan wucin gadi. Hukumar tace an kuma maida makarantu da dama a lardin Hama, matsugunan wucin gadi.
Sai dai iyalai da dama suna kwana a fili a cikin lambuna sabili da rashin isashen wurin kwana a matsugunan wucin gadin.
A halin da ake ciki kuma, wani jami’in Aleppo dake karkashin ikon ‘yan tawayen kasar Syria, Mohammed Abu Jaafar yace a kalla mutum guda ya mutu sakamakon bugun zuciya ranar Talata ta dalilin shakar iska mai guba.
‘Yan fafatuka da masu ayyukan ceton rayuka sun ce a kalla mutane saba’in aka yiwa jinyar matsalar lumfashi a birnin Aleppo, bayan abinda masu aikin ceton rayuka suka ce harin hayaki mai guba da dakarun gwamnati suka kai.
Kungiyar kare al’ummar Syria tace jirage masu saukar angulu sun jeho garewani da dama dauke da gubar "chlorine" a unguwar al-Sukkari dake karkashin ikon ‘yan tawaye.