Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Ya Isa Saudi Arabiya Domin Tattauna Batun Ukraine


Marco Rubio da Yarima Muhammad bin Salman
Marco Rubio da Yarima Muhammad bin Salman

Sakataran Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya fada a ranar Litinin cewa, Amurka na fatan ganin an warware batun dakatar da taimako agaji ga Ukraine, yayin tattaunawa a yau Talata tare da jami’an Ukraine a birnin Jeddah na kasar Saudiyya.

Rubio ya ce Amurka tana cikin yanayin sauraro kuma tana da niyyar fahimtar irin abin da Ukraine za ta iya bayarwa.

Rubio ya shaida wa manema labarai cewa “’Yan Ukraine sun riga sun karbi dukkan bayan tsaro na sirri yayin da muke magana. Ina tsammanin duk ra’ayi na dakatar da taimako gaba daya wani abu ne da nake fatan za mu iya warwarewa. Babu shakka, ina ganin abin da zai faru gobe zai zama mai muhimmanci ga hakan.”

Rubio ya ce, ba zai gindaya musu wasu sharrudan abinda dole sai sun aiwatar ba. Ya kara da cewa, yana ganin za su saurara su ga iya gudun ruwan su, daga nan sai a kwatanta da abinda Rasha ke so, bayan haka sai mu ga inda muka rarraba bisa gaskiya.

Kamar yadda ma’aikatar cikin gida ta sanar, Rubio ya jaddada kudurin shugaba Trump na kawo karshen yakin nan bada jimawa ba, ya kuma jaddada cewa, dole ne duk bangarorin biyu su dauki matakan samar da zaman lafiya mai dorewa a yayin wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Juma’a da ministan harkokin wajen Ukraine Andril Sybiha.

A ranar Litinin shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya ziyarci masarautar Saudi Arabia inda ya gana da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman a Riyadh. To amma mai yuwuwa ba zai halarci tattaunawa da jami’an Amurka ba a ranar Talata.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG