“Wannan shugaban, Donald Trump, da gwamnatinsa sun bai wa wannan fifikon. Kun ga abin da shugaban ya fada a ranar 5 ga Maris ga Hamas, inda ya bayyana karara cewa daukar 'yan kasar Amurka ko wani ‘dan kasa bisa zalunci bai dace ba kuma za a mai da martai ta hanya mafi tsauri. Don haka, an fara sabon zamani, na yi imani cewa sabon abu ne inda muke cewa ba a yarda da shi ba a kowane hali a rike 'yan Amurka a kasashen waje bisa kuskure. "
A cikin watan farko na wa'adin mulki na biyu na Shugaba Trump, an sako wasu Amurkawa 11 da aka yi garkuwa da su ko kuma wadanda aka tsare ba bisa ka'ida ba, ciki har da Marc Fogel, wanda aka daure a Rasha, da Amurkawa biyu da ake tsare da su a Gaza, biyu a Belarus, da kuma shida a Venezuela.
Daraktan Hukumar Bincike ta Tarayya, Kash Patel, wanda a baya ya shiga aikin ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin da yake aiki a Hukumar Tsaro ta Kasa, ya ce, “Babu wata hukuma da ta yi hakan. Za mu yi aiki tare da abokan aikinmu a cikin CIA da Intelligence Community. Kuma za mu rusa duk wani cikas na siyasa da ke kan hanya.”
“Alƙawarin da na yi muku a cikin wannan yanki shi ne cewa zan yi duk abin da ya kamata a matsayin darektan ku na FBI don shirya abubuwan da ake bukata don tabbatar da cewa babu wani dangin Amirka da ke jin wannan ciwo. Har yanzu ba mu samu kawo kowa ba. Ko wace irin doka da muke da ita a FBI za mu yi kokari a ko yaushe (24/7, 365) don tabbatar da cewa mun fitar da wannan adadin kuma mu tabbatar mun hana wasu shiga cikin yanayin da aka sani sosai yanzu. "
Babban mai ba da shawara Boehler ya bayyana cewa, "Wannan shugaban ba shi da damuwa game da yin amfani da ayyuka idan ya cancanta, kuma za mu mara masa baya a kan hakan. Shugaban kasar zai ci gaba da matsawa har sai an dawo da dukkan Amurkawa, matattu ko a raye."
Wannan sharhi ne da ke nuna ra'ayoyin Gwamnatin Amurka.
Dandalin Mu Tattauna