A kasar Brazil ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa gocewar laka da safiyar jiya Asabar a kusa da birnin Rio de Janeiro, ya kashe mutane 10 da raunata wasu 11, haka kuma mutane hudu sun bace, a cewar hukumomi a Brazil.
A cewar Roberto Robadey, na ma’aikatar dake kula da irin wannan masifu, bayan kwashe kwanaki biyu ana tafka ruwan sama an ayyana dokar ta baci a birnin Niteroi. Ya kara da cewa an bukaci mutane su nemi mafaka.
Haka kuma masu ceto sunce ruwan saman ya yi sanadin rarake ‘kasan wani katon dutse wanda ya afkawa gidaje da wuraren sana’a. masu aikin ceton dai na ci gaba da neman mutanen da laka da baraguzan gidaje ya rufesu.
Gocewar laka da ambaliyar ruwa wani abu ne da aka saba gani a kasar Brazil, yawancin lokuta yakan shafi yankunan da gidajen masu karamin karfi suke, saboda irin yadda aka gine-gine a kan tudu da kwari.
Facebook Forum