Hukumomi kasar Pakistan, sun saki wata macce Kirista Asia Bibi daga gidan yari a birnin Multan, bayan wanke ta da akayi daga zargin yin sabo.
Hukumomin sun tabbatar da cewar tabar gidan yarin jiya Laraba, kuma ta hau jirgi don zuwa wani wurin da ba’a bayyana ba. Hukumomin sun kara da cewar an boye inda zata ne saboda kariyar lafiya ta.
Shima lauyanta, Saif-ul-Malook, wanda ya arce zuwa Netherlands, ya tabbatar da sakin nata amma shima yace bai san inda take ba.
Tun a ranara 31 ga watan jiya ne, kotun kolin kasar Pakistan, ta watsar da hukuncin kisa da aka yanke mata a shekarar 2010, bayanda aka zargeta da yin kalaman batanci ga Manzon Rahama Annabi Muhammad (SAW).
Facebook Forum