Wannan na daga bayanan da ministan ya gabatar a taron zantawa na zauren noma na shugaban Najeriya a Abuja.
Abubakar Kyari ya baiyana cewa da duk manoma sun san arzikin da ke cikin noman alkama abun da za su tsaya a kai kenan.
Kazalika ministan ya ce ya zama mai muhimmanci a kawo iri mai inganci don samun yabanya mai yawa ya na mai misali da yanda a dan karamin fili kadada biyu a ke samun ton 10 na masara a Masar.
Babban manomi Alhaji Isa Tafida Mafindi da ke cikin mahalrta taron ya `ce in an yi amfani da kwararru za a cimma wannan nasarar mussamman daidai lokacin da shigo da abinci daga ketare ke shafar farashin albarkatun noma na cikin gida.
Taron ya ba da shawarar tallafawa manoma da na’urorin noma masu amfani da hasken rana wajen noman rani, ba da lamuni mai saukin biya da kuma sayan amfanin gonan daga hannun manoman.
Dandalin Mu Tattauna