Rasha ta yi watsi da zarge-zargen da Amurka da Burtaniya su ka yi na cewa masu kutse ta yanar gizo dake samun goyon bayan Rashar na fadada kutsensu akan kamfanoni, ayyukan gwamnati da kuma cibiyoyin Amurka da Burtaniya.
Mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya ce “ba mu san dalilin da ya kawo wadannan zarge-zargen ba.” ya fada wa ‘yan jarida a lokacin wani taron manema labarai da aka saba yi cewa, Burtaniya da Amurka basu bada wasu hujjoji ba, ya kuma yi watsi da zarge-zargen a matsayin marasa tushe.
Wannan gargadin ya zo ne daga ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka, da kuma hukumar bincike ta FBI da cibiyar tsaron yanar gizo ta Burtaniya, sun kuma hada da bada shawara akan abin da kamfanoni zasu iya yi don kare kansu.
Facebook Forum