Kimanin ton miliyon takwas na robobi ne suke karewa a cikin teku a fadin duniya a kowace shekara, amma wani tuntube a dakunan bincike na kimiyya ya baiwa masana kimiya kwarin gwiwan shawo kan wannan barazana ga duniya.
Masu bincike a Amurka da Birtaniya sun ce sun kirkiri wani sanadari bisa kuskure, wanda zai iya narkar da roba cikin gaggawa fiye da sinadarin da ake amfani da shi wurin narkar da ita a yanzu.
Sun cimma hakan ne ta hanyar kara karawa sinadarin-guba da ake kira "amino acid" da turanci da nufin rage kaifinsa, amma sai akasin haka ya faru.
Masu binciken sun ce burinsu shine su kara yin kwaskwarima ga abunda suka ganon, ta yadda za'a rika narkar da roba kwatankwacin aikin masana'antu wajen kere-kere.
Facebook Forum