Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Hezbollah Ta Kai Sabon Hari Kan Isra'ila


Kungiyar Hezbullah ta harba jerin makaman roka zuwa yankin arewacin Isra’ila a yau Alhamis, inda ta ci gaba da musayar wuta da dakarun Isra’ila a dai dai lokacin da fargabar kazancewar yaki ke karuwa.

Ana dai fargabar barkewar yaki ne bayan fashewar wasu na’urorin sadarwa a kasar Lebanon, wadanda suka hallaka akalla mutane 32 tare da jikkata fiye da wasu 3,000.

Ga alama fashewar na’urorin sadarwar ta kawo karshen hakon da Isra’ila ta jima tana yi na ganin ta kai harin kwaf daya kan mambobin Hezbullahi da dama. Tsawon fiye da kwanaki 2 a jere, na’urorin sadarwar samfurin “pager” da na oba-oba da kungiyar Hezbullah ke amfani dasu suna fashewa, inda suka raunata tare da gurgunta wasu daga cikin mayakanta, harma da illata wasu farar hula dake da alaka da rassan kungiyar tare da hallaka akalla yara 2.

Sai dai ba’a fayyace yadda harin ya dace gargadin da shugabannin Isra’ila suka rika yi a makonni baya-bayan nan na cewar zasu zafafa kai hare-hare akan kungiyar Hezbillah, runduna mafi karfin makamai a kasar Lebanon.

Gwamnatin Isra’ila ta bayyana cewa manufarta a yakin shine kawo karshen musayar wuta akan iyaka tsakaninta da kungiyar dake samun goyon bayan kasar Iran domin bada dama ga dubun dubatar Yahudawa su koma gidajensu dake yankin kan iyaka.

A jawabinsa ga dakarun Isra’ila a jiya Laraba, Ministan Tsaron Kasar Yoav Gallant yace, “mun fara bude sabon shafi a wannan yaki-ana bukatar jarunta da jajircewa da kuma juriya.” Bai ambace batun fashewar na’urori ba sai dai ya yabawa ayyukan rundunar sojin Isra’ila da sauran hukumomin tsaro, inda yace “sakamakon yana da matukar kayatarwa”.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG