Harin da kungiyar, da Iran ke marawa baya, ta kai a ranar Alhamis na daya daga cikin mafi girma a rikicin da aka kwashe watanni ana gwabzawa a kan iyakar Lebanon da Isra'ila.
Sojojin Isra'ila sun ce an harbo "makamai masu linzami da kuma wasu munanan hare-hare ta sama" kasarsu daga Lebanon, wadanda aka tare yawancinsu.
Kawo yanzu dai babu rahoton asarar rayuka.
A ranar Laraba ne Isra’ila ta dauki nauyin kashe Mohammad Naameh Nasser, jagoran daya daga cikin sassan yankuna uku na Hezbollah a kudancin Lebanon, a ranar Talata.
Sa'o'i kadan bayan haka, kungiyar Hezbollah ta harba rokoki da dama cikin arewacin Isra'ila da kuma yankin Golan Heights na Siriya da ta mamaye. Ta harba wasu rokoki a ranar Alhamis din nan, ta kuma ce ta aika da jiragen sama marasa matuka masu fashewa.
Amurka da Faransa na ci gaba da yin kame-kame don hana fadan da ake gwabzawa, wanda suke fargabar zai iya mamaye yankin.
Rikicin dai mai karamin karfi ya fara ne jim kadan bayan barkewar yakin a Gaza. Hezbollah ta ce tana kai wa Isra'ila hari ne domin nuna goyon bayanta ga Hamas.
-AP
Dandalin Mu Tattauna