A wata takardai bayani na hadin gwiwa da su ka fitar da daren Asabar, Ministocin Harkokin Wajen kasashen Amurka da Faransa da Italiya da Jamus da Burtaniya da kuma manyan wakilan kungiyar Tarayyar Turai, sun jaddada bukatar Rasha ta goyo bayan matakai na jinkai, ta daina kai hare-haren bama-bamai a Siriya, a kuma sabunta yinkurin cimma yarjajjeniya.
Taron kawayen ya kuma sake jaddada kudurinsa na wargaza kungiyar ISIS, sannan ya yi kira ga Rasha cewa ita kuma sai ta mai da hankali kan yakar al-Kaida da kungiyoyin da ke da alaka da ita a Siriyar.
Da Burtaniya da Faransa da Amurka sun kira taron gaggawa na Kwamitin Sulhun MDD da safiyar jiya Lahadi don tattaunawa kan tashin hankalin.
Sakatare-Janar na MDD Ban Ki-moon ya fadi ranar Asabar cewa ya yi takaicin abin da ya kira, "kazancewar yaki mai tayar da hankali" a birnin Aleppo da yaki ya daidaita a kasar ta Siriya, wanda shaidu su ka ce sojojin Siriya da na Rasha masu goyon bayansu ne ke izawa.