A daren jiya kuma 3 a zanga-zangar da ake yi a birnin Charlotte da ke jihar Carolina (Karolaina) ta Arewa, game da boren kashe wani bakar da ba a ga alamar ya bijirewa umarnin ‘yan sanda ba.
Daruruwan masu zanga-zangar sun bijirewa dokar ta bacin da aka saka ta hana zirga-zirga a garin, ta yadda suka ci gaba da zanga-zangarsu. Su kuma hukumomi sun ce ba zasu tarwatsa sub a matukar zanga-zangar ta ci gaba da zama ta lumana.
Wasu hotunan bidiyo sun bayyana, inda suke nuna wasu masu zanga-zangar da sassafe a yau, suna ta musabaha tare da fara’a da wasu daga cikin dakarun National Guard da ke lura da yanayin zanga-zangar.
Gwamnan jihar Karolaina ta Arewar, kuma tsohon Magajin Garin na Charlotte Pat McCrory, ya kakaba dokar ta baci a garin, tare da cewa ‘yan sanda zasu damke duk wani wanda ya saba dokar.
Mutane daga bangarori da daman a jahar sun hallara a wannan zanga-zangar, ciki har da Cherrell Brown, wata ‘yar rajin kare rayuwar bakaken fatar Amurka ta Black Lives Matter.
Wacce ta baro Greensboro da ke makwabtaka da birnin don yin mubaya’a ga wannan zanga-zangar da ake ci gaba da gudanarwa har zuwa yau.