Shugaban Kasar Falasdinu Mahmoud Abbas ya fadawa babban zauren majalisar dinkin duniya a ranar Alhamis cewa, cigaba da mamaye yankin yammacin kogin Jordan da Isra'ila ke yi ya ruguza kyakykyawan zaton kawo mafita a kai ruwa ranar da ke tsakanin kasar Yahudawa da kuma makotansu kasashen larabawa.
Abbas yace, “Abinda Gwamnatin Israila ke yi na fadada mazauninsu ya ruguza yiwuwar kawo mafitar da ta ragewa kasashen guda biyu na kan iyaka tun shekarar 1967."
Firaminista Netanyahu yayi watsi da maganar Abbas inda yace a shirye suke da a tattauna domin samun matsaya, amma abu daya da ba zai taba yadda a tattauna akai ba shine samun 'yancin kasa daya tilo ta Yahudawa.
Netanyahu ya gayyaci Abbas da ya zo ya tattauna da 'yan majalisar Isra'ila a Knasset, shi kuma a madadin haka shima zai yi magana kai tsaye da 'Yan majalisar Falasdinawa
A baya Falasdinawa sun yi burus da irin wannan gayyata da Netanyahu ya yi musu inda suka bayyana cewa tsatstsauran ra’ayinsa kan muhimman abubuwa su suka hana yiwuwar tattaunawarsu.