A ranar 18 ga watan Disambar shekara ta 2014 ne taron kolin Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York ya amince da ayyana kowacce ranar 13 ga watan Yuni ta kasance ranar gangamin wayar da kan al’ummar Duniya dangane da muhimmancin mutunta masu dauke da larura ta Zabiya, farawa a shekara ta 2015.
Gabanin hakan sai da hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta zartar da wani kudiri dake neman bada kariya ta musamman Zabiyan mutane, daga tsangwama da kuma nuna kyama a wasu sassan duniya.
Ciwon zabiya dai wani ciwo ne da ake gadonsa daga haihuwa, kasancewar matsalar wani sinadari da ake samu a jiki wanda ke taimakawa ana samun bakin jiki. Wasu mutane basu da wannan sinadari a jiki wasu kuwa suna dashi amma sai dai kadan ne.
Dakta Umar Faruk Abdullahi, yace Zabiya mutane ne kamar kowa banbanci da za iya gani shine a fatarsu, inda jikinsu ke zama fari tas, haka kuma gashin kansu ya zama ruwan dorawa sai kuma idanunsu dake zama wata kala da daban.
Domin karin Bayani.