Kamar yadda shugaban hukumar agajin gaggawa ta Najeriya Sani Cidi, ya bayyana a ganawarsa da tawagar kula da agajin gaggawa da jin kai ta Afirka AU, yace ta hanyar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya aka cimma wannan yarjejeniyar dawo da ‘yan gudun hijirar.
Don yiwuwar mayar da su garuruwansu na asali da hadin gwiwar gwamnatocin jihohinsu da suka fito, musamman ma Borno da Yobe da Adamawa.
Sani Cidi bai fadi lokacin da za a fara kwaso mutanen ba, sai dai yace za a tabbatar an ‘dauko su bisa ra’ayin kansu da kuma mutunta bukatunsu da samar da inda za a tsugunnar dasu bisa ma’ana, koma a samu a mayar da su muhallansu na asali.
Komishiniyar hukumar agajin gaggawa da jin ‘kai ta kungiyar Afirka Aisha Laraba Abdullahi, tace alkalumansu sun nuna akwai wadanda suka rasa matsugunnansu wanda suke zaune a sansanoni a Najeriya su Miliyan 13, haka nan akwai ‘yan Najeriya Miliyan 3 da sukayi gudun hijira zuwa ketare.
Domin karin bayani.