Tuni majalisar dattawan Najeriya ke kokarin samarda hukumar raya jihohin arewa maso gabas da rikicin ya rutsa dasu.
Sanata Abubakar Abba Ibrahim dan majalisar yace kowa ya san irin abubuwan da suka faru a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa. Idan ba wata hukuma ta musamman aka kafa ba ta taimakawa wuraren da wuya su farfado. Bandasu akwai sauran jihohin a yankin da su ma suka dandana rikicin Boko Haram. Duk suna bukatar taimako da kulawa.
Yace yadda aka yiwa Niger Delta haka yakamata a yiwa arewa maso gabas yadda duk shekara suna cikin kasafin kudin kasar.
Shi ma Usman Alhaji Ibrahim daya daga cikin mutanen da rikicin ya raba da gidajensu yace idan an kafa hukumar ta duba halin da suka shiga a yankin su taimaka masu saboda Allah. Da an gyara masu wurarensu zasu yi kwadayin komawa.
Kwamitin shugaban kasa kan farfado da yankin a karkashin Janar Theophilus Danjuma yace suna bukatar akalla nera tiriliyon biyu da miliyan dari biyu wajen sake gina yankin lamarin da ya sa sanatoci irinsu Muhammad Hassan suka ce sai an yi hukuma sukutum guda.
Ga karin bayani.