Tun lokacin zabe kasa ta rabe kashi biyu inda 'yan arewa da Yarbawa suka dauki bangare daya su ka mutane Igbo da 'yan kudu kudu suka dauki nasu bangaren.
Yace tun rabewar aka ga watarana irin abun dake faruwa yanzu zai faru. Maganin irin wannan rabewar da tun farko an kirasu a kafa gwamnatin hadin kai. Hakan bai faru ba har aka kafa gwamnatin da bangare daya ya mamaye.
Ana iya gyara idan an sake kiransu su zo da wakilansu a zauna dasu aga yadda za'a tafiyar da gwamnati tare. Yace ba zasu yadda a tafiyar da gwamnati basu ciki kuma daga wurinsu ake diban mai da kasar ta dogara a kai.
Matukar 'yan arewa suna siyasa ba ilimi, suna siyasar san rai to ko ba za'a samu cin gaba ba. Dole a bi shawarar masu ilimi, masu fahimta ba bin shawarar 'yan gari ba, kuma a ce duk abun da suka so shi za'a yi. Wannan kasa tana bukatar a kira kowane bangare a zauna tare domin a yi tafiya tare. Kada a kula da siyasar da ta raba kasa.
Idan ana son masalaha a kira manyan shugabannin kowane bangare a zauna tare a tattauna a shirya yadda za'a tafiyar da gwamnati. Yin hakan ne zai kawo zaman lafiya. Amma idan an ce za'a cigaba yadda ake tafiya yanzu ana bi ana kama mutanen to muna yaudarar kanmu ne. Ko shakka babu zasu cigaba da tawayen.
Ga karin bayani.