Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafindi ya kalubali Falana akan barazanar kai gwamnatin Buhari kara


Shugaba Buhari da Mataimakinsa Farfasa Osinbajo suna nazari kan kasafin kudi
Shugaba Buhari da Mataimakinsa Farfasa Osinbajo suna nazari kan kasafin kudi

Farkon wannan makon ne shahararen lauyan nan mai rajin kare hakkin bil'Adama yace Shugaba Buhari bashi da hujjar ciwo bashi daga China, maimakon hakan ya karbi kudaden da kamfanin NNPC ya rike tare da kwato wadanda mutane suka wawure daga gwamnati.

A ganin Femi Falana kwato kudaden da aka sace da tilastawa kamfanin NNPC biyan kudaden da ya ki ya saka cikin asusun gwamnatin tarayya su ne suka fi a'ala ba ciwo bashi daga China ba.

Da Mafindi yake mayarda martani yace kasafin kudin da aka yi bana za'a yi anfani da nera tiriliyon biyu domin biyan bashin cikin gida da ake bin gwamnati. Yace duk kasashen duniya na zuwa China karbar bashi. Ko Amurka China na binta dala tiriliton hudu.

Idan China ta ba Najeriya bashi ba kudi muraran zata kawo ta ba Najeriya ba. Zata shigo da kwararru da kayan da suke kerawa su kerasu a Najeriya sannan su karantar da mutanen kasar yadda zasu kera kayan..Kudaden da Najeriya ta kwato suna nan amma duk abun da kasar zata saya dole ne ta biya tsaba.

Mafindi ya yadda Femi Falana kwararran lauya ne amma bai san kan tattalin arziki ba ko yadda ake saka jaki. Haka kuma bai san yadda ake cin bashi a duniya ba.

Bashin da shugaba Buhari zai karbo zai bude wasu hanyoyi da dama da kasar zata anfana dasu, rayuwa kuma ta inganta. Yayi misali da layin dogo da za'a gina ya kewaye kasar. Yace zai sa daukan yaka daga kudu zuwa arewa ya zo da sauki.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG