Akwai labariin cewa an sake tafka wasu kura-kurai a cikin kasafin kudin da aka mikawa shugaba Buhari domin ya sanya hannu.
A cewar Kawu Sumai’ila, a halin da aka ciki kasancewar kasafin kudin nada yawan shafi da ya kai 1800, hakan ne yasa har yanzu ana ta dubawa ana kididdige shi domin tabbatar abinda aka aika da kuma gyara-gyaran da akayi cikin sa kafin a fitar da matsaya guda daya.
Har yanzu dai ba a kammala aiki kan kasafin kudin ba, Kawu Suma’ila dai yace ana sa ran gobe idan Allah ya kaimu za a yi kokarin kawo karshen wannan bita da akeyi daga nan kuma a san matsaya. Idan har akwai wasu manya manyan canji da aka samu to za mayarwa da majalisa kasafin domin su yi bayani kan canje-canjen da suka yi.
Saurari sautin hirar.