Ministan ya kira kungiyar ta yi aiki kafada da kafada da hukumomin gwamnati dake sa ido a lamarin samar da man fetur a kasar domin tabbatar da cewa an samu mafita mai dorewa.
Ministan man fetur Dr. Emmanuel Ibe Kachukwu ya kafa wani kwamiti na mutum goma sha hudu da suka hada da mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur ko IPMAN Alhaji Abubakar Maigandi Dakingari.
A wata fira da Alhaji Dakingarin ya yi da Muryar Amurka yace kungiyarsu a shirye take ta hada kai da gwamnati domin shawo kan matsalar man fetur nan bada jimawa ba.
Yace ministan ya basu tabbacin zai basu jirgi daya daga cikin jirage shida da zasu shigo da mai. Za'a basu dama su shigo da mai tare da basu dala akan farashen gwamnati.
Shi ma dan kwamitin amintattu na kungiyar dillalan man Alhaji Baba Kano Dada ya ba shugaba Muhammad Buhari shawara. Yace da yake gwamnati ke samar da kashi tamanin cikin dari na man fetur da ake samar ma kasar bai kamata a samu matsala ba muddin gwamnati ta samu kwararru su yi aikin. Idan kuma man ya shigo kamata ya yi a hada kai da kungiyar IPMAN kan yadda za'a rabashi.
Ga karin bayani.