Jam'iyyar APC dake jagorantar sauran jam'iyyun adawa a jihar Taraba ta kira wani taron manema labarai inda ta bayyana kukansu.
Ta kira taron ne na niyyar mayar da martani kan wasu manufofin gwamnatin jihar da tace basa kan ka'ida ko dokokin kasar gaba daya. 'Yan adawan sun fitar da wata wasikar koke da suka rubutawa shugaba Buhari akan abun da suka kira mulkin kama karya da yake wakana a jiharsu.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar yace zasu cigaba da sa ido akan gwamnatin jihar kan duk abun da tayi ba daidai ba. Sun bukaci shugaba Buhari da ya hanzarta ya kafa kwamitin bincike game da batun korar wadanda ba 'yan asalin jihar ba ne da suka ce gwamnatin jihar na shirin yi.
To saidai talakawa na kokawa game da halin kuncin rayuwar da suke fama dashi a kasar inda su 'yan jam'iyyar APC ke cewa jama'a su hada da hakuri. Shugaban APC na jihar yace mutane sauri su keyi. Ba zata yiwu ba a gina gida rana guda. Ya dorawa jam'iyyar PDP alhakin matsalar da kasa ta samu kanta yau. Ya kira 'yan jam'iyyar da su ilimantar da mutane kada su bari wasu su rudesu.
Gwamnan jihar ya mayar da martani da bakin hadiminsa Mr. Sylvanus Giwa. Ya kwatanta zargin da APC keyi da shure-shuren banza wanda bashi da kai ko gindi. Yace duk wanda bashi da aikin yi sai ya sa kansa a wani halin banza da wofi kamar wanda bashi da ilimi. Yace yaya za'a yi a ce wata jiha tana korar wasu zuwa ina?
Ga karin bayani.