Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Yi Aiki Da Kasashen Turai Duk Da Rashin Fahimtar Da Ake Samu


Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley.
Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley.

Wakiliyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Nikki Haley, ta fada jiya Talata cewa Amurka zata yi aiki da sauran kasashen Turai, duk da rashin fahintar da ake samu nan da can lokaci-lokaci a tsakanin juna.

Ta ce kar wani ya fassara wannan dan banbancin manufofi ya zamo wata alama ce ta sabani tsakanin kasashen na Turai, tace wannan amincin dake tsakanin mu mai karfin gaske ne. Halley ta furta hakan ne a sailin da take jawabi ga kwamitin sulhu na MDD.

Haley ta kira NATO a matsayin babban ginshikin hadin kan kasashen na Turai, tace yanzu haka ma Amurka na kokarin ganin ta tabbatar ta kara karfi fiye da yadda take ada.

Wadannan kalaman nata dai sun kara jaddadawa ga wadanda mataimakin shugaban kasar na Amurka, Mike Pence yayi a ranar littini, wanda ya shaidawa Sakataren na NATO Jen Stoltenberg, cewa Amurka a shirye take ta bunkasa wannan kawance, sai dai kawai sauran kasashen na bukatar bada gudunmowar kudi domin tabbatar da inganta matakan tsaro dai-dai wadaida.

‘’Mun kuduri aniyar ganin mun kara adadin abinda muke kashewa a harkar tsaro, mu dai a Amurka zamu taka namu rawar, Karkashin shugabancin Donald Trump inji Pence,Sai dai ya kara da cewa yanzu lokaci ne na aiwatar da kalamai a aikace ba batu ne na fatar baka kawai ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG