Rahotanni daga jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya na cewa jami’an hukumar yaki da sha da fataucin muggan kwayoyi ta Najeriya, NDLEA, sun samu nasarar bankado wasu muggan kwayoyi da kudinsu ya kai naira miliyan ashirin da aka boye cikin indomi.
Kama kwayoyin na zuwa ne yayin da shan muggan kwayoyi a tsakanin matasa ke kara habaka a Najeriya.
Wannan nasarar da jami’an hukumar ta NDLEA suka samu ta biyo bayan wani samame da suka kai wani wuri da ake hada-hadar sayar da muggan kwayoyin kuma cikin wadanda suka kaman har da 'yan mata da kuma masu sayar da madarar sukudayi.
Mr Yakubu Kibo shine kwamandan hukumar ta NDLEA a jihar Adamawa, yace yanzu haka wadanda ke safarar muggan kwayoyin kan sauya salo ta hanyar amfani da kayayyakin masarufi ko boyewa a cikin abinci inda har suka gano wasu sundukan tramadol da wasu kwayoyi da kudinsu ya kai naira miliyan ashirin da aka cusa a kwalayen Indomi.
Haka nan Yakubu Kibo, yace wadannan kwayoyin maye akan ma ketara da su zuwa kasashen ketare don samun kazamar riba.
Facebook Forum