A yau alhamis rundunar sojojin Najeriya zata fara gudanar da rawar daji a jihohin Binuwai da Taraba, a wani matakin shawo kan barazanar tsaro da ake fuskanta da sunan rikicin makiyaya da manoma a wadannan jihohin.
Wannan rawar dajin da aka lakaba wa suna "Ayem Akpatuma" zata kuma kunshi jihohin Nassarawa, Kogi, Neja da kuma Kaduna, a cewar babban hafsa mai kula da aikace-aikace da kuma atusayen a hedkwatar rundunar sojojin Najeriya, Manjo janar David Amadu.
Wakilin Muryar Amurka, Hassan Maina Kaina, yace wannan rawar daji ta musamman da sojojin shiyya ta daya da shiyya ta uku zasu gudanar tare da sa hannun birged ta masu gadin fadar shugaban kasa da ma zaratan sojojin birged ta 707, zata nemni shawo kan sace mutane, fashi da makami, fadace-fadace da dai sauran abubuwan dake barazana ga tsaron kasa a wadannan yankuna.
Janar Amadu yace, wannan rawar daji ta zamo dole a saboda yadda " fashi da makami, da satar mutane da satar shanu da suka yi katutu a Jihar Neja," da "Miyagun laifuffukan da ake aikatawa a jihar Kogi" da kuma uwa uba "Rikice-rikicen makiyaya da manoma da kashe-kashen da 'yan daba ke yi a jihohin Binuwai, taraba da Nassarawa."
Yace wannan babbar barazanar tsaro ce wadda dole sojoji su sanya hannu domin shawo kansu.
Kakakin rundunar sojojin Najeriya, Birgediya-janar Sani Kukasheka Usman, ya fadawa wakilinmu cewa za a yi amfani da wannan dama domin jaddada kwarewar sojojin da zasu yi wannan aiki, tare da magance wasu matsalolin tsaro da suka addabi wadannan wurare.
Facebook Forum