A jawabinsa wurin kaddamar da jirgin leken asirin, shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmancin rawar da sojoji ke takawa wurin samar da kyakkawar yanayin samar da ci gaban kasa.
Shugaba Buhari yayi amfani da jawabin nasa ya jinjinawa dakarun Najeriya bisa jajircewarsu na karya lagon Boko Haram. Shugaban da yake cike da farin ciki, yace wannan kurman jirgi da yake kaddamarwa wani abin alfahari ne, ganin yanzu sojojin saman Najeriya sun kai ga cimma wannan fasaha da zata kara karfafa sha’anin tsaro.
Babban hafsan sojojin saman Najeriya, Air Marshal Sadik Abubakar, ya tabo kadan a cikin abubuwa da jirgin ya kunsa.
Yace, jirgin mai suna, “Tsegumi” na da tsawon mita biyar da digo daya, yana kuma da nauyin kilogram 50, wanda kuma ke hade da na’urar daukar hoto mai fasahar hasken Infrared a jikinsa, watau zai iya hango mutum ko a cikin duhu, ko a cikin hadarin ruwan sama, kuma yana iya tashi ko sauka a hanya mai tsawon mita dari uku, kana yana zuwa leken asiri kamar nesan kilomita dari, sa’annan yana ganin abinda ke sama da nisan taku dubu goma sha biyar kana yana aikinsa na tsegumi har na tsawon sa’o’i goma ba kakkautawa.
Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshal Sadik Abubakar, yace koda baya ga wannan sun cimma nasara da dama musamman a fannin jiragen.
Facebook Forum