An kama wasu mutane da suka sauya akalar kayan abincin da aka ware domin 'yan gudun hijira a Bauchi
Kayan abincin an dauko su ne daga Kaduna zuwa Bauchi duk da cewa akwai rubutun da ke cewa ba na sayarwa ba ne.
An sauke kayan ne a wata Unguwa a Bauchi inda aka fara sauya buhunan abincin zuwa na kasuwa, abin da ya sa mutanen unguwar suka farga suka kuma koka.
Malam Umar Musa Shehu shugaban 'yan gudun hijira na jihar Bauchi ya ce akwai abincin da aka kawo daga wani yankin yammacin Afirka kuma an rubuta cewa ba na sayarwa ba ne.
Da aka tambayi masu sauya buhun sai suka ce su ma sun saya ne daga Kaduna.
Kawo yanzu dai an mika mutanen hannu 'yan sanda har ma an kama wasu da suka sayo kayan wadanda watakila su ba da bayanan da zai kai ga kama ainihin masu shirya wannan cuwacuwar.
Saurari rahoton Abdulwahab Muhammad domin karin bayani.
Facebook Forum